Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Oduaghan ta yi zargin cewa, jami’an tsaron Najeriya su na yunkurin kama ta idan ta dawo Najeriya.

Natasha ta ce hakan yana da nasaba da zuwanta taron IPU da ya gudana a birnin Niyok ɗin ƙasar Amurka, inda ta yi ƙorafi dangane da dakatar da ita da kuma zargin cin zarafi ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio.
A zantawarta da jaridar Premium Times ta wayar tarho jiya Lahadi, Natasha ta ce tana sane da shirin da ake yi na kama ta da zarar ta dawo Najeriya.

Sanatar da har yanzu tana ƙasar ta Amurka, ba ta faɗi ko wacce rundunar tsaro ce ke kitsa kama ta ba.

Idan za a iya tunawa dai hukumomin Najeriya na ciki da waje tuni sun hau kan bincike, akan ta yadda aka yi ta samu damar halartar taron ba tare da samu gayyata a hukumance ba.