Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka ƴan ta’adda mutane 31, waɗanda su ka addabi yankunan jihar Katsina.

Cikin wasu hare-hare guda biyu da rundunar ta kai, ta cimma wannan gagarumar nasarar ta tarwatsa ƴan ta’addar.
Harin farko dai ya gudana ne ƙarƙashin rundunar Operation Fansar Yamma, inda su ka samu nasarar hallaka ƴan ta’adda mutane 12 ciki har da shugabansu mai suna Dogo.

Lamarin ya auku ne a ƙauyen Maigora da ke ƙaramar hukumar Faskari, wanda ya zamo sanadiyyar mutuwar mutane biyar daga cikinsu tun da farko.

Sai hari na biyu kuma da ya auku dukka dai ƙarƙashin rundunar ta Operation Fansar Yamma, inda su ka yi wa ƴan ta’addar luguden wuta ta sama.
A harin an samu nasarar hallaka ƴan ta’addar 19 a yankunan Unguwar Goga da Ruwan Goɗiya a ƙaramar hukumar ta Faskari, waɗanda dukkansu yaran ƙasurguman ƴan ta’addar nan ne Alhaji Gero da kuma Alhaji Riga.
Rahotanni su bayyana cewa dai rundunar tsaron su na ci gaba da sanya ido a yankin, dan tabbatar da ƴan ta’addar ba su sake haɗewa waje guda ba.