Attajiri na ɗaya a nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirinsa na gina tashar jiragen ruwa da kuma faɗaɗa samar da siminti a jihar Ogun.

Yayin tattaunawarsa da muƙarraban gwamnatin jihar Ogun a jiya Litinin, Dangote ya shaidawa gwaman jihar Dapo Abiodun wannan yunƙurin na sa.
Ya ce kamfaninsa zai samar da tashar jiragen ruwan da ta fi kowacce girma a ƙasar, a shiyyar harkokin kasuwanci ta Olokola.

Ɗan kasuwar ya kuma bayyana cewa yanzu haka ana kan ginin manyan masana’antun samar da siminti guda biyu, a yankin Itori da ke jihar.

Gwamnan jihar Abiodun ya yi farin ciki da jin wannan ci gaban, inda ya ce haɓaka samar da simintin zai mayar da jihar ta Ogun matakin farko wajen samar da simintin a yankin Sahel.
Inda kuma ya ce ba su da kalaman da za su godewa attajirin ɗan kasuwar, bisa yadda ya ke cigaba da fito da ƙimar Najeriya a idanun duniya.