Majalisar wakilan Najeriya ta musanta zargin da ake yi mata na karbar cin hanci kafin amince da ayyana dokar tabaci da shugaba Bola Tinubu ya sanya a Jihar Rivers.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanar da dan Majalisar mai wakiltar Mazabar Gwaram ta Jihar Jigawa Hon Yusuf Shitu Galambi ya fitar a yau Asabar.
Galambi ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin zarge-zargen da ake yi musu na karbar cin hancin kafin amincewa da ayyana dokar, ko kuma matsa musu su amince da ita.

Sanarwar ta bayyana cewa mafiya yawa daga cikin ‘yan Majalisar sun goyi bayan ayyana dokar ne don kare martabar dimkradiyya tare da tsare burukan a’ummar Jihar.

Acewarsa ‘yan Majalisar sun amince da ayyana dokar ne bisa kishin kasa da kuma hadin kan siyasa, zaman lafiya, tare kuma da kare dimkradiyyar Kasar.
Galambi ya ce yayi matukar mamaki da yadda ake yada irin wannan jita-jitar na matsawa ‘yan Majalisar wajen karbar cin hanci kafin amince da sanya dokar.
Akarshen dan Majalisar ya yi kira ga ‘yan Kasar da su sani cewa ‘yan Majalisar na yin aiki ne don samar da daidaito kafin karewar wa’adin dokar.