Kungiyar Amnesty Internationan ta ce wajibi ne a yi bincike kan zargin da sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha ta ke yi wa kakakin majalisar dattawa.

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin bayani dangane da lamarin.
Ƴan jam’iyyun adawa a ƙasar sun caccaki lamarin ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya Atiku Abubakar.

A cewar jam’iyyar PDP ta zargi kakakin majalisar da take haƙƙin sanatar bayar ƙin amincewa da buƙatarsa.

A wata sanarwa da Amnesty Internationan ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan tsare-tsare Isa Sanusi, kungiyar ta yi kira ga mahukunta a ƙasar da su gaggauta yin bincike a kan lamarin.
A cewarsu bai kamata a ci gaba da tafiya a haka ba yayin da majalisar ta yi watsi da zargi tare da nuna rashin kulawa a kai.
A cewar ƙungiyar ta ce zargin babban hatsari ne ga al’ada wanda sannan danne haƙƙi ne don samar da adalci.
Sanata Natasha dai ta yi zargin kakakin majalisar dattawa da yunƙurin lalata da ita da kuma cin zarafinta
