Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da tserewar wasu Fursunoni a Jihar bayan fasa wani gidan gyaran hali a garin Koton-karfe da ke Jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kingsley Fanwo ya tabbatar da lamarin a yau Litinin, inda ya ce kimanin fursunoni 12 ne suka tsere daga gidan gyaran halin a safiyar yau din.
Acewar Fanwo gwamnatin za ta tabbatar da ganin cewa ta yi hadin gwiwa da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu hanyar tserewar.

Kwamishinan ya kuma nuna damuwarsa akan lamarin, yana mai cewa tserewar fursunonin abin tambaya ne duba da cewa babu wata alama da ta nuna yadda aka yi suka tsere.

Fanwo ya ce gwamnatin Jihar za ta gudanar da bincike mai zurfi, don gano wadanda ke da hannu wajen tserwar ta su, tare da kuma da kama fursunonin.
Akarshe ya bukaci al’ummar Jihar da su bai’wa jami’an tsaro hadin kai, tare da ba su rahoto dukkan wani abu da suka gani ba su yadda dashi ba, don ganin an kamo, inda ya ce dukkan wanda aka kama da bai’wa fursunonin mafaka zai fuskanci hukunci.
