Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranakun da daliban makarantun Firemare da Sacondry na gwamnatin Jihar za su koma makaranta.

Daraktan wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano Balarabe Abdullahi Kiru ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da masu zaman kansu za su koma makarantunsu a gobe Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025.

Yayin da ya ce ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa za su koma makarantunsu a ranar Litinin 7 ga wata na Afrilu.

Sanarwar ta yi kira ga iyayen daliban da su kula sosai wajen ganin yaran su sun koma makaranta akan lokaci.
Kwamishinan Ilimi na Kano Dr Ali Haruna Makoda ya ja kunnen ɗaliban da su kaucewa shiga da miyagun abubuwa cikin makaranta irin reza,wuƙa, ko kuma kwayoyi, yana mai cewa gwamnatin Juhar za ta ɗauki mataki akan dukkan ɗalibin da aka kama da karya doka.