Alamu na nuni da cewar farashin man fetur na iya faduwa ƙasa a Najeriya bayan da farashin gangar mai ya fadi a kasuwar duniya.

A halin yanzu ana siyar da gangar mai dala 65 saɓanin dala 69.90 da ake siyarwa a baya.


Wannan na zuwa ne bayan da kamfanonin mai su ka ƙara farashin lita a Najeriya.
Wasu gidajen mai a Najeriya na siyar da kowacce lita kasa da naira 900, sai dai sun ƙara farashin a yan kwanakin nan.
Matatar mai ta Dangote ta sanar da ƙara farashin man da take siyarwa da yan kasuwa tun kwanakin baya.
Sakamakon faduwar farashin gangar mai a kasuwar duniya ana kyauta zaton farashin man fetur na iya faduwa kasa a Najeriya.