Hedkwatar tsaro ta Kasa ta musanta rade-raden da ke yawo cewa an biya kudin fansa kafin kubtar da tsohon shugaban Hukumar masu yiwa Kasa hidima ta NYSC Janar Mahrazu Tsiga mai ritaya.

Daraktan yada labaran hekwatar Janar Tukur Gusau, ne ya musanta batun a jiya Litinin ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Hedkwatar ta ce ba gaskiya ba ne rade-raden biyan kudin fansa kafin kubtar da Tsiga daga hannun ‘yan bindiga.

Sanarwar ta bayyana cewa tun bayan yin garkuwa da Mahrazu Tsiga da masu garkuwa suka yi, jami’an tsaron sojin suka dukufa bin dazuku domin ganin an kubtar da tsiga daga hannun Maharan.

Acewar sanarwar nasarar kubtar da Tsiga ta samu ne bayan hare-hare da jami’an suka matsa da kai’wa cikin dazuka, wanda hakan ne ya bayar da damar cetoshi shida sauran mutane da maharan suka sace tsawon lokaci.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: