Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta samu nasarar kubtar da wasu mitane Bakwai da ‘yan bindiga suka yi yunkurin sacewa a Kauyen Kurba da ke cikin karamar hukumar Kankara a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Abubakar Sadik Aliyu ne ya bayyana hakan a jiya Talata, a yayin ganawa da manema labarai.
Sadik ya ce jami’an ‘yan sanda hadin gwiwa da na Sa-kai ne suka samu nasarar.

Kakakin ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda na karamar hukumar Dutsan-Ma ne, suka kai daukin gaggawa a lokacin da maharan suka yi garkuwa da mata Biyar.

Bayan samun rahotanni akan yunkurin na maharan a ranar Litinin jami’an suka yi gaggawar kai dauke tare da ceto matan, bayan yin musayar wuta.
A wani bangaren kuma kakakin ya ce jami’an sun kuma sake samun nasarar kubtar da wasu mutane biyu mace daya namiji daya, a wata musayar wuta da suka yi da ‘yan ta’adda bayan sun kai hari Kauyukan Gidan Filoti, da gidan Mairabo a Karamara hukumar Malumfashi ta Jihar.