Jami’an rundunar sojin Najeriya na ‘Operation Safe Haven, sun gano gawar wani makiyayi mai suna Abdullahi Muhammad mai shekaru 16 da aka nema aka rasa , tare da ƙwato shanu fiye da 50 da aka sace a Jihar Filato.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa jami’an sojojin sun gano gawar matashin makiyayin ne, tare da wasu Fulani makiyaya a yau Juma’a.
Rahotanni sun ce shanu sama da 70 ne aka sace a yankin Ariri da ke cikin Karamar hukumar Bassa ta Jihar a lokacin da suke gudanar da kiwo a yankin.

To sai dai Babban Sakataren kungiyar raya Irigwe IDA Danjuma Auta ya musanta rahotan satar shanu a yankin, inda ya zargi cewa an hallaka mambobinsu da dama a cikin makonni uku da suka gabata, inda kuma suke fuskantar kalubalen hare-hare a yankin.

Shima shugaban Ƙungiyar fulani makiyaya ta MACBAN na garin Bassa Ya’u Idris ya tabbatar da nasarar gano gawar makiyayin , yana mai cewa jami’an tare da wasu makiyaya ne suka gano gawar a wani kabari mara zurfi, a gabar kogi da ke kusa da yankin Ariri, inda kuma an cire kan makiyayin da hannunsa na hagu.