Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina haɗin gwiwa da jami’an soji da DSS sun hallaka ƴan bindiga biyar a jihar.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar yau Juma’a.
Ya ce jami’an sun kwato babura guda bakwai wanda ƴan bindigan ke kai hare-hare a kansu.

A cewar sanarwar, an hallaka yan bindigan a jiya a ƙauyen Dutsen Wori da ke ƙaramar hukumar Dandume a jihar.

A dai wannan rana ta Alhamis sun kuma samu nasarar kama wasu masu kai wa yan bindiga bayanai su uku.
An kama mutanen ne a unguwar Adam da Unguwar Judo da ke ƙaramar hukumar Danmusa a jihar.
Sannan an kwato babura guda biyu.
Kafin kama waɗanda ake zargi sai da aka yi musayar wuta da yan bindiga.
Kwamishinan yan sanda a jihar ya yabawa jami’ansa bisa ƙoƙarin da su ka yi.
Sannan ya bukaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron haɗin kai wajen basu bayanai da za su taimaka musu a aikinsu.