Ƙungiyar jagororin arewa ta League Of Northern Democrats ta yi Allah wadai da kisan mutane 52 da ba su ji ba ba su gani ba a ƙaramar hukumar Bokkos da ke jihar Filato, inda ta bayyana kisan a matsayin rashin imani tsantsa.

Ƙungiyar ta kuma bayyana kaɗuwarta, dangane da ƙara tsamarin rashin tsaro a yankunan Bokkos da Mangu da ke jihar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar Dr. Ladan Salihu ya fitar a yau Asabar, sun buƙaci gwamnatocin tarayya da na ƙananan matakai da su shawo kan matsalar da ta ta’azzara a yankin.

Ta kuma yi kira da a gaggauta ɗaukar matakin gurfanar da hukunta waɗanda su ka aikata laifin, tare da buƙatar gwamnati na da ta tabbatar da an yi adalci.

Ƙungiyar ta kuma yi addu’a da bayyana jaje da goyon bayanta ga al’umma da gwamnatin jihar ta Filato, da kuma iyalan wadanda abun ya rutsa da su.

A ƙarshe ta yi gargaɗin cewa rashin shawo kan matsalar tsaro a jihar ka iya mayar da yankin wata matattara ta rikici a ƙasar, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da duk wani abu da ake buƙata don samar da tsaro da kawar da zubar da jini a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: