Wasu Rahotanni daga Jihar Filato sun bayyana cewa an hallaka wani uba da ‘ya’yansa biyu a Kauyen Zogu da ke Miango a cikin Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar.

Mai magana da yawun Ƙungiyar ci gaban Irigwe IDA Sam Jugo ne ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a garin Jos.
Jugo ya ce mutanen da aka hallaka sun hada da Weyi Gebeh mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da kuma Henry Weyi mai shekara 16.

Kakakin kungiyar ya ce an kashe uba da ‘ya’yan nashi ne a cikin dare a lokacin da suke tsaka da yin bacci, yana mai bayyana lamarin a matsayin rashin na dabbanci.

Acewar an sanar da shugabannin Ƙungiyar ci gaban Irigwe IDA faruwar lamarin na Kauyen Zogu, Miango wanda ya yi sanadiyyar hallaka uba da ‘ya’yansa nasa biyu, inda ya ce wannan harin na baya-bayan nan ya kai ga hallakar mutane tara a cikin makon nan kaɗai.
IDA ta kuma nuna damuwarta akan kara ta’azzarar matsalar rashin tsaro a yankin Irigwe, inda ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi dukkan abin da ya dace domin kawo karshen matsalar da kr faru a yankin, da kuma kama masu aikata laifin domin ganin sun fuskanci hukunci.
Sai dai bayan faruwar lamarin ba a samu ji daga jami’in hulda da jama’a na rundunar Operation Safe Haven ba Manjo Samson Zhakom, da kuma kakakin rundunar ’yan sandan jihar DSP Alabo Alfred bayan aike musu da sako.