Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ba shi da wani yunkuri na ficewa daga jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar SDP.

Ndume ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a ta cikin shirin Politics Day na gidan Talabijin na Channels.

Acewar Sanatan ba shi da wani shiri na komawa wata jam’iyyar Kasar, duk kuwa da yadda ake yada cewa wasu manyan jam’iyyar ta APC na shirin ficewa daga cikinta.

Kazalila Ndume ya bayyana dalilin da ya sanya wasu fitattun ‘yan jam’iyyar APC ke shirin ficewa daga cikinta, inda su na yin hakan ne sakamakon rashin kulawa da bukatunsu ko kuma sanya su a cikin sha’anin gwamnatin da suka dafa wajen ganin an kafa ta.

Har ila yau ya ce gaza biyawa ‘yan jam’iyya bukatunsu hakan ne ke sanyasu gaza zama guri guda, a cikin jam’iyyu.

Ndume ya kara da cewa Jam’iyyar APC na iya shiga cikin damuwa matukar zargin da ake yi ya tabbata na komawar wasu ‘yan jam’iyyar cikin SDP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: