Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa dukkan wata dunkulewa waje guda da jam’iyyun adawa a Kasar nan za su yi, hakan ba zai sanya jam’iyyar APC ta gaza samun nasara ba a zaben 2027 da ke tafe.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan ne a yau Asabar a Jihar Kaduna a lokacin da ya jagoranci shugabannin jam’iyyar ta APC wajen kai’wa tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari ziyara a gidansa da ke Jihar ta Kaduna.

Ganduje ya ce dukkan wata hadaka jam’iyyun Kasar nan za su yi hakan ba zai yi tasiri ba, akan jam’iyyar APC.

Shugaban ya kara da cewa ziyarar da Tsohon Mataimakins shugaban Kasa Alhaji Atikun Abubakar da wasu tsofaffin gwamnonin Kasar nan suka kai’wa Buhari, ba ta tayarwa da jam’iyyar hankali ba, duba da cewa su na son kulla wata alaka wadda ko kadan ba za ta taba yin tasiri ba.

Har ila yau Ganduje ya kara da cewa sun shirya tsaf, tare da yadda za su bullowa lamarin, inda ya ce ba zai ce komai ba akan abunda za su.

Ganduke ya bayyana cewa a halin yanzu Jihohi 21 na Kasar nan na karkashin mulkin APC, yana mai cewa har yanzu jam’iyyar na kallon karin wasu Jihohin, inda ya ce ko wasu gwamnonin Jihohin da ba APC ba ce take mulkarsu su dawo jam’iyyar ta APC, ko kuma Jihohin su dawo karkashin Ikon APC ta hanyar gudanar da zabuka.

Sannan Ganduje ya bayyana cewa sun ziyarci Tsohon shugaban ne domin bayyana masa i irin nasarorin da kuma ci gaban da jam’iyyar APC ta samu tun bayan barinsa kan karagar mulkin Kasar, tare da kuma tabbatar masa da kudirinsu na ci gaba da ayyukan don ganin jam’iyyar ta ci gaba da samun nasara.

Ganduje ya kara da cewa za kuma su dunga sanar da Buhari irin halin da jam’iyyar ke ciki.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: