Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya ce zai tuntuɓi takwaransa na jihar -Kano Abba Kabir Yusuf, domin yanke shawarar akan kuɗin diyya da za a biya iyalan mafarautan da aka kashe a garin Uromin jihar.

A jiya Juma’a sakataren yaɗa labaran gwamnan Fred Itrua ya ce, za a cimma matsaya a tsakanin gwamnatocin jihohin biyu, kuma za a bayyanawa jama’a matsayar da aka cimma.

A yayin da ya ke karɓar wata tawagar wakilai a ranar Alhamis Okpebholo ya ce, gwamnatin tarayya bisa haɗin guiwa da gwamnatin jihar ta kafa wani kwamitin da zai yi duba da yanayin da mummunan al’amarin ya faru.

Okpebholo ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru a Uromi ba, kuma ya ƙuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar don kowa ya samu damar yin rayuwa tare da kasuwancinsa.

Gwamnan ya kuma ce tawagar wakilan gwamnatin Kanon sun kai masa rahoto, kuma iya gwamnatin ta Edo ce ta ke da wannan rahoton.

A ƙarshe ya ce za su duba buƙatun da gwamnatin Kanon ta bijiro da su, tare da cewa za kuma su tuntuɓi gwamnan na Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: