Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yana nan yana shirye-shiryen ka’wa tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari ziyara a gidansa da ke Kaduna.

Ndume ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a wata hira da Channesl TV ta cikin shirin Politics Today.

Acewar Ali Ndume zaiyarar da ake kai’wa tsohon shugaban, ba wani abun mamaki ne duba da cewa na daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasa, da ke da martaba musamman a yankin Arewa.

Ndume ya ce zai ka’iwa Buhari ziyara ne bisa radin kansa, inda ya ce alakar da ke tsakaninsa da Buhari ta wuce ta siyasa.

Sanatan ya bayyana cewa nan bada dadewa zai ziyarci muahmmad Buhari, yana mai cewa kai’wa tsofaffin shugabannin Kasa ziyara ba sabon abu ne a Kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: