Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta bayyana cewa, ta hallaka mutane huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da su ka addabi yankunan Ogwashi-Uku da kuma Ubulu-Uku.

Mai magana da rundunar SP Bright Edefe ne ya bayyana hakan, yau Asabar a garin Asaba babban birnin jihar.

Edefe ya ce biyo bayan sace wani likita ne a yankin Isele-Uku a watan Afrilun da muke ciki, kuma ba a sake shi ba sai da aka biya diyyar Naira miliyan 15 tare da direbansa.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Olufemi Abaniwonda ya umarci jami’ai na musamman da su gudanar da bincike, don tabbatar da an kamo waɗanda ake zargi tare da hukunta su.

Biyo bayan umarnin nasa ne kuma jami’an suka aiwatar da sumame jiya Juma’a tare da kama wani mai suna Abubakar Usman, wanda ake zargin shi ne jagoran masu aikata laifin.

Ana zarginsu ne dai da hannu wajen yin garkuwa da wasu manyan mutane da sauran al’umma, a yankunan Ogwashi-Uku, Ibusa, Ubuluku.

Edafe ya ce sumamen nasu ne yayi nasarar kama masu laifin a maɓoyarsu a jiya Juma’a, da ke dajin kan babbar hanyar Asaba/Agbar.

Mai magana da yawun rundunar ya ƙara da cewa, an garzaya da waɗanda su ka samu ciwo zuwa asibitin Ogwashi-Uku, kafin daga bisani a tabbatar da mutuwarsu baki ɗaya.

Ya kuma ƙara da cewa rundunar ta samu nasarar gano kayayyaki da suka haɗar da bindiga ƙirar AK47 guda uku, da kuma abubuwan fashewa guda 90.

Leave a Reply

%d bloggers like this: