Hukumar shirya Jarrabawar shiga manyan Makarantu ta JAMB a Najeriya ta sanar da ranar Alhamis mai zuwa 24 ga watan Afrilun da muke ciki a matsayin ranar da za a fara rubuta jarrabawar ta shekarar 2025, maimakon ranar 25 ga watan na Afrilu da saka tun da fari.

Mai magana da yawun hukumar Dr Fabian Benjamin ne ya tabbatar da hakan a yau Asabar ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce an canja ranar rubuta jarrabawar ne domin ganin muhimman matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tanadin sauran hukumomin da za su tallafa mata a yayin gudanar da aikin rubuta jarrabawar.

Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katinsu na shiga jarrabawar da ke ɗauke da bayanai akan jarrabawar.

Benjamin ya kuma ce a cikin katin akwai bayanan gurin rubuta jarrabawar da kuma lokacin da mutum zai rubuta jarrabawar da kuma sauran dukkan bayanai akan jarrabawar a jikin katin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: