Shugaban jam’iyyar APC a Najeriya Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai ƙarin wasu gwamnoni da za su sauya sheka daa jam’iyyun su zuwa jam’iyyar APC.

Ganduje ya bayyana haka ne a gidansa da ke Abuja, yayin da ya karbi manyan ƴan jam’iyyar NNPP da wasu jam’iyyu wanda su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
A cewar Ganduje, sun gamsu da irin salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma tsarin da ya ɗauka kan tattalin arzikin ƙasa

Sannan ya bayar da misali da jihar Edo wanda su ka yi takara tare da lashe zabe a jihar.

Da yake amsa tambaya dangane da batun wasu gwamnoni da ke shirin komawa jam’iyyar APC, ganduje ya tabbatar da haka wanda ya ce tabbas wasu da dama na hanyar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Ganduje ya karbi wasu jiga jigai a jam’iyyar NNPP wanda su ka hada da Sanata Kawu Sumaila, Babba Bichi, Kabiru Alasan Rurum da kuma Shaaban Sharada daga jam’iyyar ADP da wasu da dama wanda su ka koma jam’iyyar APC.