Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu akan dokar kirkiro da sabbi hukumimo hudu a Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
Hukumomin da gwamnan ya bayar da umarnin samarwa sun hada da Hukumar Kare Hakkokin mutane ta Jihar Kano KASPA, da Hukumar Kula da Allunan Tallace-tallace KASIAA, Hukumar yada labarai da Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamani KASITDA, da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaita Masana’antu KASMEDA.

Sanarwar ta ce samar da sabbin hukumomin zai tallafawa harkokin kananan sana’o’i da kirkire-kirkire, tsara tallace-tallace, da kuma kare hakkin al’umma da samar da ayyukan yi.

Gwamnan ya ce hukumomi za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, janyo masu zuba hnnun jari, da bunkasa tsare-tsaren gwamnati, don ganin Jihar ta samu bunkasar tattalin arziki da kuma ci gaba.
Sannan gwamnan ya ja kunme akan karya sabbin dokokin, inda ya ce za a hukunta dukkan wanda aka kama da karya su da kuma tsauraran matakai domin tabbatar da bin doka da oda.