Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutane 13 da ake zargi da zubar da ciki, tare da mutuwar wata yarinya mai shekaru 18 a Jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Ahmad Wakil ne ya tabbatar da hakan.

Kakakin ya bayyana cewa rundunar na zargin wasu mutanehuɗu daga cikin mutanen da aka kama da aikata laifin fyade, da kuma zubar da ciki da mutuwar Matashiyar yarinyar a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau ta Jihar.

Kakakin ya kara da cewa tun a ranar ranar 4 ga watan Afrilun da nuke ciki, rundunar ta samu bayanai kan cewa akalla watanni hudu da suka shude, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun yiwa wata yarinya fyade.

Acewarsa daga lokacin da suka gane yarinyar na ɗauke da juna biyu, suka nemi wani mutum tare da ba shi naira 40,000, don ya zubarwa da yarinyar cikin, wanda yayi silar mutuwarta.

Wakil ya ce bayan samun rahoton lamarin sun samu nasarar kama wadanda ake zargi, tare da amsa laifinsu, da kuma zayyo wadanda ke da hannu a cikin lamarin.

Wakil ya ce a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike, bayan kammalawa kuma za a gurfanar da su a gaban kotin domin girbar abinda suka shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: