Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa, babu wani ƙage ko ɓata suna da zai kawo zaman lafiya a jihar Rivers.

Wike ya bayyana cewa idan ana son wanzar da zaman lafiya a jihar dole sai dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da ƴan majalisar wakilai sun haɗa kai da shigowa ciki da nufin kawo gyara.
Ya kuma ƙara da cewa cewa ayyana dokar ta ɓaci a jihar ya yi daidai, kuma ya dakatar da afkuwar wasu bala’ai da za su iya faruwa a jihar.

Nyesom Wike dai ya yi dukkan wannan kalami ne a wajen bikin zagayowar ranar haihuwa ta cika shekaru 70 a duniya, na tsohon dan majalisar wakilai Ken Chikere jiya Juma’a a birnin Fatakwal ɗin jihar Rivers.

Wike ya ƙara da cewa yawaitar gudanar da zanga zanga ba zai dawo da zaman lafiya ba, inda ya soki shugabannin gargajiya da sauran masu mulki, tare da cewa sun ɗauki ɓangare dangane da rikicin siyasar da ya ke faruwa a jihar.
Ya ce sarakunan ba su yi wani yunƙuri wajen yin sasanci a tsakanin ɓangarorin da su ke taƙaddama ba.
A ƙarshe ya ce zaman lafiya zai dawo jihar ne kaɗai idan an samar da sasanci na gaskiya ga ɓangarorin biyu, ba tare da sanya wani ra’ayin siyasa ko buƙatar wani rukuni ba.