Gwamnatin Jihar Kano ta bankaɗo wata almundahana da aka yi yayin biyan albashin ma’aikata na watan Maris ɗin da ya gabata, inda ta gano cewa har yanzu ana biyan mutane 247 waɗanda ko dai sun mutu ko kuma sun bar aiki, inda kuɗin almundahanar da ake biyansu ya kai Naira miliyan 27, 824, 395.40.

Hakan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da jami’in yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnati Musa Tanko ya fitar a yau Asabar.
Ya kuma ƙara da cewa an binciko ayyukan ba daidai ba yayin binciken da aka yi, wanda kwamitin bibiyar biyan albashi ya gudanar.

Tanko ya ƙara da cewa an samu nasarar ƙwato kuɗaɗen, kuma tuni aka mayar da su zuwa asusun ƙananan hukumomi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin a shirye ta ke don ganin ta tsaftace tsarin biyan albashin, da kuma ɗaukar mataki akan waɗanda su ka aikata ba daidai ba.
Ya kuma ce kwamitin zai ƙaddamar da ayyukansa nan ba da daɗewa ba, wanda zai ƙunshi dukkanin masu ruwa da tsaki don gamsashshen bibiyar tsarin biyan albashin.
Ya kuma ce za a gudanar da ƙarin bincike don gano yadda lamarin ya yi tsamari da kuma waɗanda suka aikata, don girbar abinda su ka shuka ta fuskar doka.