Wani hadimi ga gwamnan Jihar Delta Harrison Gwamnishu ya tabbatar da ajiye mukaminsa bisa wasu dalilai nasa.

Hadimin gwamnan ya ajiye aikin nasa ne ta cikin wata wallafa da ya fitar a jiya Juma’a.
Acewarsa ya ajiye aikin ne bisa matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a Jihar, wanda hakan ya sanya ya dauki matakin hakan.

Ya kara da cewa tun tuni ya yi kokarin janyo hankalin gwamnan kan samar da hanyoyin da za a kawowa Jihar mafita, amma hakan ya gagara.

Hadimin gwamnan ya ce gwamnatin Jihar ko kadan ba ta shirya daukar matakai na magance matsalar rashin tsaro ba, wanda hakan ya sanya ya gaza yin aiki cikin gaskiya da amana.
Harrison ya bayyana cewa bayan yin zuzzurfan nazari ne ya sanya ya dauki matakin ajiye aikin.