Wasu da ake zargin ƴan ta’addan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai wani hari tare hallaka mutane shida, ƙasa da mako guda a ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

A wannan karon ma sun kuma kai wani harin da yammacin jiya Asabar zuwa ƙauyen Kwapre dukka dai a ƙaramar hukumar ta Hong da ke jihar.
Ana kyautata zaton cewa maharan ƴaƴan ƙungiyar ta’addancin Boko Haram ne, wanda su ka kai harin tare da hallaka mutane 10 cikin ƴan sintirin tsaron garin tare da jikkata wasu da dama.

Ɗaya daga cikin dattijai kuma jagororin garin ya shaida cewa, sun rasa mutane goma daga cikin haziƙan mutanen su, wasu kuma su na can su na ƙoƙarin tsira da rayuwarsu a garin na Hong.

Tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti a cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke cikin garin na Hong don samun ɗaukin gaggawa, kamar yadda wani ɗan siyasa a garin mai suna Hyella Anthony ya tabbatar.
Ɗaya daga cikin wanda ya ganewa idonsa abin ta’ajibin Hyella Anthony ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa yawan hare-haren da ake kaiwa yankin ya yi yawa matuƙa.
Ya ce ƴan bindigar sun je ne da yawan gaske ɗauke da makamai, inda su ka ci karimin ƴan sintiri masu bayar da tsaro a garin tare da hallaka mutane 10 a cikinsu, sauran da su ka raunuka kuma aka garzaya da su asibiti.
A nasa jawabin hakimin Dugwaba Simon Yakubu ya bayyana baƙin cikinsa game da yawan faruwar hare-haren, inda ya ce wannan shi ne karo na biyar da aka kai hari a ƙauyukan da ke yankin a ƙasa da makonni biyu.