Rundunar ƴan sandan jihar Oyo ta bayyana cewa ta gano shirin ayyukan safarar bil’adama birnin Badin na jihar, tare da samun nasarar tseratar da mutane 83 da abin ya shafa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Adewale Osifeso ne ya tabbatar da hakan, yayin zantawarsa da manema labarai.

Adewale ya ƙara da cewa waɗanda aka ceto ɗin sun haɗar da maza 57 da kuma mata 26, cikinsu kuma har da jarirai.

Ya kuma ƙara da cewa yanzu haka su na ci gaba da gudanar da bincike dangane da lamarin, kuma za su sanarwa da al’umma halin da ake cike idan binciken na su ya kammala.

An ruwaito cewa an tseratar da mutanen ne dai a wani gini da ke yankin Oregun a birnin na Badin, inda ake zargin an ɓoye su na tsawon wani lokaci.

Wata majiya da ta buƙaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa mutanen ƴan asalin ƙasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ne, inda aka kawo su Najeriya bisa dalilan ƙarya da yaudara na samar musu da ayyukan yi.

Majiyar ta ƙara da cewa masu safarar mutanen sun karɓi maƙudan kuɗaɗen Dalolin Amurka a wajen iyayensu da ƴan uwansu, bisa tsarin zamba da kuma yaudara

Leave a Reply

%d bloggers like this: