Hukumar hasashen yanayin sararin samaniya ta Najeriya NiMET ta yi hasashen samun tsawa da yanayin hazo a faɗin Najeriya, daga yau Lahadi zuwa ranar Talata mai zuwa.

A cikin rahoton ta na yanayi da ta fitar jiya Asabar a birnin tarayya Abuja, NiMet ta yi hasashen samun madaidaicin yanayin hazo mai ɗauke da ƙura a jihohin Katsina, Sokoto, Zamfara, Borno, Kano, Yobe da jihar Jigawa.
Ta kuma yi hasashen samun tsawa a wasu yankunan jihohin Adamawa da Taraba a dukkan rahotannin da ta fitar.

A yankin Arewa ta tsakiya kuwa NiMET ta yi hasashen samun hadari da safe sai kuma tsawa da rana zuwa yamma, a jihohin Filato, Kogi, Nasarawa, Benue da kuma birnin tarayya Abuja.

A kudancin ƙasar nan kuwa ta yi hasashen samun tsawa da safe a wasu yankunan jihohin Legas, Cross River, Rivers, Bayelsa da kuma Akwa Ibom.
A ranar Talata kuwa NiMET ta yi hasashen samun buɗewar rana da gajimare a jihohin Arewa, da kuma samun tsawa da safe a jihohin Adamawa da Taraba.
Hukumar ta kuma ja hankalin al’umma da su ɗauki matakan kariya yadda ya kamata, sakamakon za a iya samun iska mai ƙarfin gaske ta biyo bayan ruwan sama a jihohin da ka iya fuskantar yanayin tsawa.
