Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya naɗa hadimai 168 domin cigaban gwamnatin jihar.

Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai Mukhtar Gidado nenya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Talata.

Daga cikin waɗanda aka nada akwai mataimaka na musamman, da kuma manyan mataimakan gwamnan, da sauran hadiman da za su taimaka masa a bangare daban-daban.

A cewar sanarwar, nadin ya faru ne domin taimakawa gwamnatin don ganin an samu bayanai cikin gaggawa na bukatar al’ummar jihar

Sannan an zabo mutanen ne daga bangare daban-daban bisa cancantarsum

Gwamnan ya taya waɗanda ya nada murna tare da kira a garesu da su jajirce wajen sauke nauyin da aka dora musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: