Rundunar sojin saman Najeriya ta gudanar da bikin yaye sabbin matuka jiragen sama 35, bayan sun kammala karbar horo a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar 401 FTS da ke Jihar Kaduna.

Babban Hafsan Rundunar Air Mashal Hassan Abubakar ne ya sanyawa sabbin matuƙan igiyoyi.
Yaye sabbi matukan 35 na zuwa ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, don ci gaba da gudanar aikin kawar da ‘yan ta’adda a fadin Kasar.

Sai dai Air Mashal Hassan ya ce a halin yanzu rundunar na jiran na jiran karin sabbin jiragen yakin 34.

A yayin taron yabuƙaci daliban da aka yaye da su kasance masu amfani da damar wajen yin aiki tukuru domin kawo karshen batagari a fadin Najeriya.