
A yau majalisar ɗinkin duniya ta amince a yi biki don tunawa da irin gudunmawar da ƴan jarida ke bayarwa a cikin al’umma, da kuma ƙalubalen da aikin ke ciki musamman ta fuskar ƴancin furtawa ko zaƙulowa. Kira ga gwamnati don bai wa ƴan jarida ƴanci da kuma wayar da kan al’umma a kan muhimmancin ƴancin ƴan jarida na daga cikin manufa ta ware wannan rana.
Aikin Jarida – Shi ne kawo labari na gaskiya don sanar da halin da ake ciki a ɓangare daban-daban kuma ta fuska da dama. Ginshiƙi shi ne aiki domin al’umma yadda za a amfanar da jama’a da kuma taimakawa wajen samar da haɗin kai da zaman lafiya da cigaba ga al’umma.

Ƴancin Jarida ko Ƴancin Ƴan Jarida – Da yawan wasu da ke kiran kansu da ƴan jarida sun siyar da ƴancinsu da kansu, e ƙwarai, sun siyar da ƴancinsu da kansu wannan maganar na taɓa faɗa a shekarun baya kuma hujjoji da dalilai sun sake bayyana zuwa yanzu. Daga cikin wasu da ke kiran kansu da sunan ƴan jarida na yin ɗabi’u da su ka saɓa da koyarwa da kuma tarbiyyar aikin jarida.

Zargin wasu da ke saka rigar jarida su na yawon maula ko bambaɗanci tare da yin barazana ko zare ido da baza riga don a ji tsoronsu a ofisoshin gwamnati ko wajen masu hannu da shuni, hakan ya sa ake yi musu ihisani daga cikin wasu masu faɗa a ji, ofisoshin gwamnati, masu riƙe da muƙamai don gudun kada a saɓa musu.
Manufar hakan ita ce idan aa ƙi, su kuma su yi amfani da damarsu wajen fito da wani gurɓataccen hali ko badaƙala da su ka sani amma su ke rufa-rufa saboda wannan ihisani.
Wasu kuwa sam ba ma su da ƙwarewa a aikin, su na amfani da damar da su ke da ita ne ta, wataƙila ko don saboda mabiya da su ke da shi ko ƙarfin faɗa a ji sakamakon fakewa da sunan aikin jarida.
Yayin da wasu ke amfani da damar don tunanin azurta kansu, saboda fifita buƙatarsu ko son zuciyarsu, sun fi fifita kuɗi a kan gaskiya, sun mayar da aikin zallar kasuwanci ba tare da yin maƙasudi ko jigo a cikin aikin ba.
A kan yi amfani da wasu da ke kiran kansu ƴan jaridar don ƙaryata gaskiya duk da cewar kuwa sun san cewar abinda su ke faɗa ba haka ba ne. Misali, wata jaridar ko ɗan jaridar ya tono wani abu da ake zaluntar al’umma, sai a yi amfani da su wajen rufe labarin, ko yi masa kwaskwarima tare da wanke ɓangaren da su ke goyon baya. Idan kuwa za a yi haka anya za a iya ƙwatar ƴancin da ake fafutuka ƴan jarida na da shi kuwa? Idan fa baki ya ci dole ido ya ji kunya.
Irin wannan ne ke sa jami’an tsaro cin zarafin ƴan jarida.
Ƴan siyasa su ke wulaƙanta ƴan jarida.
Masu faɗa a ji ke kyarar ƴan jarida.
Idan al’umma su ka rasa ƴan jarida yayin da aka samu gurɓatattu a cikin shugabanni, jami’an tsaro, malamai, alƙalai da lauyoyi to ina za su kai ƙwarin gwiwarsu kuma?
Makomar Jarida ko Makomar aikin jarida a yanzu – Da yawan wasu ƴan jarida na iya rasa aikinsu saboda barinsu a baya wajen tafiya da zamani. A halin da ake ciki kafafen sa da zumunta na zamani sun fi ƙarfin faɗa a ji a kan sauran kafofin yaɗa labarai na baya da su ka shahara kuma aka sani.
Sauka daga manufofin aikin jarida da kuma rungumar son zuciya, wasu wasu da ba ƴan jarida ba na iya yin aikin kuma a kirasu da ƴan jarida.
Matuƙar ba a yi da gaske ba wajen ci gaba da neman hanyoyin tafiya da zamani, to kuwa babu shakka za a raba wasu ƴan jaridar da aikinsu, misali waɗanda za su karɓe ragamar tafiyar da shi za su zama ba ƴan jarida ba, kuma saboda ƙarfi da za su yi a ɓangaren ya zama wajibi a bi su.
Ƴan jaridan za su kasance koma baya amma ga wanda ya mayar da kansa baya domin a halin da ake ciki babu wani abu da ke da tasirin kafofin sa da zumunta wajen isar da saƙo ko ina kuma cikin ƙanƙanin lokaci.
Rashin iya ƙirƙirar abubuwan da za su yi don kawo cigaba tare da kwaikwayo a kan wanda ya ƙirƙira ko kuma nuna lalaci wajen gudanar da aikin.
KIRANA – Ƴan jarida su san kansu, ta yadda za su ci gaba da riƙe kambun da aka basu na amanar al’umma wajen fito da zahirin abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma tare da sauke nauyin da ke wuyansu musamman a cikin al’umma. Bayyana gaskiya komai ɗacinta da kuma kaucewa duk wani abu da ka iya kawar da hankalinsu daga zahirin aikin, Allah ne mai azurta bawansa.
FATANA – Aikin jarida ya ci gaba da zama misali idan za a yi kwatancen gaskiya da riƙon amana, kwarjibinsa ya dawo jikin waɗanda su ke yin sa bin haƙƙi da gaskiya.
Daga ƙarshe akwai wasu da ke zama karen farauta da sunan masu magana da yawun wasu, su kan shiga riga ko komar aikin jarida don goge gaskiya tare da lulluɓeta da ƙarya wanda hakan babbar illa ce ga rayuwarsu a gaba. Batu ne mai zaman kansa da zan yi magana kansa a nan gaba.
Abubakar Murtala Ibrahim
#Abbanmatashiya ne ya rubuta
Abbakarmurtala1@gmail.com
+2348030840149
5 Zulƙida 1446
3/5/2025