Mutane 23 ake zargi sun rasa rayuwarsu sakamakon wani sabon hari da aka kai jihar Benue.

Dangane da ƙaruwar kashe-kashen da ake samu a jihar majalisar wakilai ta yi sammacin gwamnan da gwamnan jihar Zamfara don yin bayani a kai.
Sabon harin da aka kai na zuwa bayan da majalisar wakilai ta bai wa gwamnan jihar mako guda don bayyana a gabanta dangane da hare-haren da ake kai wa wanda ke silar rasa rayukan mutane.

Ƙananan hukumomin da aka kai hare-haren sun haɗa da Guma, Kwande, Ukun da Logo.

Sakamakon harin da yawan mutanen garin sun tsallake sun gudu.
Wani shaidar gani da ido ya ce an hallaka mutane tara a ƙaramar hukumar Logo, sai mutane takwas a ƙaramar hukumar Ukum yayin da aka kashe mutane uku uku a ƙananan hukumomin Guma da Kwande.
Lamarin ya faru a ranar Juma’a yayin da yan bindigan su ka mamaye yankunan.
Zuwa yanzu jami’an tsaro da gwamnati a jihar ba su ce komai a kai ba.