Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci Rundunar sojin Kasar nan da ya sake aikewa da Jami’anta Jihar Borno da Yobe don ganin sun dakile hare-haren mayakan Boko-haram a Jihohin.

Majalisar ta bayyana hakan ne a zamanta na yau Talata, inda ta ce ta damu matuka da ayyukan ‘yan ta’adda a Kasar.
Majalisar ta bukaci hakan ne bayan kudurin da mai tsawatarwa na Majalisar Sanata Muhammad Tahir ya gabatar Monguno.

Acewar Tahir ko da a yau Talata sai da Boko-haram suka kai hari garin Gajiram Karamar hukumar Nganzai a Jihar.

Dan Majalisar ya kara da cewa a halin yanzu ‘yan ta’addan na amfani da jirage marasa matuƙi, da kuma Bom, wanda kuma hakan ke ƙara haifar da rasa rayukan jami’an soji da kuma mutae, tare da dakile yawaitar zirga-zirgar mutanen a yankin.
Idan kuma bayan yin nazari akan kudurin Majalisar ta bai’wa rundunar sojin Kasar umarnin aikewa da karin jami’an tsaro yankin Arewa Maso Gabashin Kasar, tare da kayan aiki don kawo karsen ‘yan ta’addan.
Sanna majalisar ta umurci kwamitin Majalisar kan harkokin sojin Kasa da na sama da su sanya idanu don ganin an tabbatar da ƙudirin.