Aƙalla mutane 1,593 ne su ka mutu sakamakon haɗɗuran mota a Najeriya.

Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya FRSC ce ta tabbatar da haka wanda ta ce mutanen sun mutu cikin watanni hudun farko na shekarar 2025.

Bayanan da aka tattara ya nuna an samu ƙatuwar haɗɗura da asarar rayuka da kuma waɗanda su ka jikkata.

A watannin hudun haɗɗura 2,650 aka samu a Najeriya daga watan Janairu zuwa watan Maris.

Haka kuma akwai mutane 9,298 da su ka samu rauni a sakamakon haɗɗuran wanda ya zarce mutane 8,659 da aka damu a watanni hudun farkon shekarar 2024 da ta gabata.

Rahoton ya nuna cewar an fi samun haɗɗuran a manyan titunan ƙasar da ya haɗa tsakanin jihohi.

Sannan motocin bas da tirela da manyan motoci aka fi samun haɗɗuran da su.

Dangane da ƙididdigar da kungiyar lafiya ta duniya WHO ta fitar kuwa ta gano Najeriya ne aka fi samun yawan mace mace sanadin haddura a nahiyar Afirka.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: