Fiye da ƴan ta’adda 13,000 aka hallaka a Najeriya cikin shekaru biyu .

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka jiya Alhamis a taron da aka yi domin duba irin nasarorin da gwamnatin jam’iyyar APC ta samu ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewarsa yan ta’adda 13,543 aka hallaka cikin shekaru biyu a Najeriya.

Sannan akwai yan Boko Haram da ISWAP da iyalansu su 124,408 da su ka mika wuya ga jami’an tsaro.

Sai kuma harsashin yan ta’adda 252,596 da su ka lalata.
Tun bayan bayyanar ƴan Boko Haram akwai kutane sama da 350,000 da aka kashe sai kuma sama da mutane miliyan biyu da aka raba da muhallansu kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana.
