Kungiyar Association of Zamfara North Concerned Citizens ta yi kira ga Ƙaramin Mininstan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Muhammad Bello Matawalle da ya sake tsayawa takarar gwamnan Jihar a zaben shekarar 2025 da ke tafe.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a yau Juma’a, ta cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar Muhammad Usman Moriki ya fitar.

A sanarwar da Kungiyar ta fitar ta bayyana cewa a zamanin da Matawalle ke mulkin Jihar, an samu ci gaba mai tarin yawa da Nasarori wajen yakar rashin tsaro, tare da karfafa gwiwar jami’an tsaro.

Sanarwat ta kara da cewa Matawalle ya yi abin azo a gani sosai wajen tunkarar matsalolin rashin tsaro duk da ƙarancin kudi, tun daga lokacin da ya fara mulkin Jihar har zuwa lokacin da ya kammala.

Kungiyar ta kuma soki salon yadda gwamnan Jihar mai ci Dauda Lawal ke tafiyar da salon mulkin Jihar, tana mai cewa gwamna Dauda ya gaza wajen samar da sauyi duk kuwa da ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnatinsa ke samu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a lokacin da Matawalle na gwamna a Zamfara ya samarwa da jami’an tsaro motocin aiki 200, tare da biyansu kuɗaɗan aiki na kowanne wata.

Sai dai Kungiyar ta ce gwamnatin Dauda babu wani abun a zo agani da samarwa da Jihar Zamfara tun bayan hawansa karagar mulkin Jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: