Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya bai’wa Alhazai 3,200 na Jiharsa kyautar Riyal 1,000 na Ƙasar Saudiyya wanda yayi dai-dai da naira 450,000 na Najeriya.

Gwamnan ya bai’wa alhazan Jihar ta shi tallafin ne a jiya Asabar, a ziyarar da ya kai musu a garin Minna, tare da taya su murnar kammala aikin hajjinsu cikin nasara.

Gwamna Ahmad ya ce ya basu kyautar kudaden domin tallafa musu kafin dawowarsu Najeriya, sannan kuma ya yaba musu bisa yadda suka bi dokar da Kasar ta Saudiyya ta sanya.

Kazalika gwamnan ya bukaci Alhazan da su kara kaimi wajen yin addu’o’i neman zaman lafiya a Jihar dama Ƙasa baki daya.

Har ila yau gwamnan Aliyu ya ce gwamnatinsa ba za ta gajiya ba wajen kulawa da walwala da kuma jindaɗin maniyyar jihar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: