Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta na samun nasara wajen farfaɗo da kamfanin Ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi.

Ministan Karafa Shu’aibu Abubakar Audu ne ya tabbatar da hakan a wajen wani taro da ya yi da manyan jagororin jam’iyyar APC na Jihar Kogi, a garinsu na Ogbonicha da ke cikin karamar hukumar Ofu a Jihar.
A yayin taron ministan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta sanya hannu akan a wata yarjejeniya da ƙamfanonin da za su yi aikin samar da kayan aikin Kamfanin.

Abubakar Abdu ya bayyana cewa gwamnatin na kuma ƙara neman masu zuba hannun jari daga Ƙasar China, da su sanya hannu jari a cikin kamfanin.

Sannan ya jinjinawa shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa tsare-tsaren da ya ke yi wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar farfado da harkokin sarrafa Ƙarafa a Ƙasar.