Ƙaramin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya yi kira ga gwamnan Jihar mai ci Dauda Lawal da ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Matawalle ya bayyana hakan ne a wata ziyara sallah da magoya bayansu suka kai a garinsu na Maradun da ke Jihar ta Zamfara a jiya Asabar.
Matawalle ya bukaci da gwamnan Dauda da ya koma jam;iyyar APC domin ganin Jiharsu ta Zamfara ta ci gaba a dukkan harkokinta.

Ƙaramin Ministan ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kasance jam’iyya mai kishin Ƙasa da kuma son ƴan Ƙasarta, yana mai cewa matukar gwamna Dauda nada aniyar kawowa jihar ci gaba ta bangaren tsaro, da kuma zaman lafiya, to babu shakka ya koma APC don hada kai da ’yan kwamitin ci gaban jam’iyyar ta APC.

Bello Matawalle ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya samar da zaman lafiya da ci gaban mai dorewa a Najeriya, inda kuma ya ke neman goyon bayan gwamnonin jihohi harma da sauran shugabanni a Ƙasar domin ganin ya samu nasarori.