Ministan birnin taryya Abuja Nyesom Wike ya sauya sunan babban dakin taro na Kasa da Kasa da ke Abuja wato Abuja International Conference Centre AICC, zuwa Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre.

Wike ya bayyana hakan ne a yau Talata a gurin kaddamar da sabon ginin dakin taron a Abuja.

A yayin kaddamarwar Wike ya ce an sabunta ginin dakin taron wanda yayi daidai da zamani, da ke bukatar bashi kulawa sosai.

ministan ya bayyana cewa dukkan wanda ke son gudanar da taro a dakin taron, to ya zama wajibi ya biya kudi komai mukaminsa.

Acewarsa tun a shekarar 1991 da gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida a mulkin soja ta samar ba a taba yi mata gyara ba, tun bayan samar da ita.

Wike ya ce dukkan wata wata ma’aikatar gwamnati ko hukumar da ke son yin amfani da gurin taron, zai biya kudi domin ganin an ci gaba da bai’wa gurin kulawa.

A yayin taron shugaba Bola Tinubu ne ya jagoranci kaddamar da sake bude dakin taro, bayan komawarsa Abuja daga Jihar Legas hutun sallah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: