Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya bayyana cewa matukar ba a gaggauta daukar mataki ba, Najeriya na iya komawa tsarin jam’iyyar ɗaya a zaben shekarar 2027 da zuwa.

Gwamnan Bala ya bayyana hakan ne a gurin bikin ranar Dimkuradiyya ta bana da aka gudanar a jiya Alhamis, wanda Mohammed Atiku Isah ya wakilce shi a yayin taron.

An gudanar da taron ne a Jihar Kaduna wanda kungiyar Matasa ta Young Democrats of Nageria ta shirya, tare da gayyar gwamna Bala.

A yayin taron ranar Dimkradiyya ta bana a jawabin da shugaban Kasa Bola Tinubu yayi a zauren Majalisar Tarayya musanta zargin cewa gwamnatinsa na yunkurin mayar da Ƙasar tsarin jam’iyya ɗaya.

Sai dai gwamnan na Bauchi da ke karkashin jam’iyyar PDP ya ce ya zama wajibi a dauki matakin kare tsarin jam’iyya siyasar Ƙasar daga yunƙurin mamayar wata jam’iyya guda ɗaya.

Kazalika gwamna Bala ya ce akwai babban hadari matukar Najeriya ta koma tsarin jam’iyya ɗaya a zaben 2027, ya ce hakan kuma sabawa dimkuradiyya ne.

A karshe ya bukaci ƴan Najeriya da su kasance masu sanya idanu da kuma kare ƙima da martabar dimkradiyya, da zamowa masu kare ƴancinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: