Akalla mutane 26 ne suka mutu a wasu hare-hare da ‘yan ta’adda suka kai wasu daga cikin yankunn kananan hukumomin Makurdi da Katsina Ala da ke Jihar Benue.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun hallaka mutane 25 a yankin North Bank da ke Makurdi, inda kuma mutum ɗayan ya rasa ransa a wani hari na daban da aka kai Kenvanger da Agbami a yankin Mbatyula ta karamar hukumar Katsina-Ala.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigan da zuwan ‘yan bindigan suka kutsa kai gidaje mutane daga ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na ranar Alhamis.

Sun ce maharan sunje ne dauke da bindigogi da adda da sauran wasu makaman.

Acewarsa daga cikin mutanen da aka hallaka sun hada da mata da yara, inda kuma wasu har yanzu ba a gansu ba.

Rundunar ‘yan sandan Jihar ta ce za ta fitar da cikakken bayani akan lamarin, inda ta ce tuni ta aike da jami’anta yankunan da abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: