Hukumar kula da yanayi ta Ƙasa NiMet ya bayyana cewa akwai yuwuwar samun ambaliyar ruwan sama a wasu daga cikin Jihohin Ƙasar nan.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar.
NiMet ta bayyana cewa daga cikin jihohin da barazanar ta shafa sun haɗa da Jihar Zamfara, Sokoto, Filato, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Nasarawa, Benue, Ogun, Ekiti, Rivers da kuma Delta.

Yayin da a halin yanzu Jihar Akwa-Ibom ce ke fuskantar barazanar.

Hukumar ta bukaci al’umma musamman mazauna Jihohin da aka bayyana, da yashe magudanan ruwansu, don ganin ruwa ya samu hanyar wucewa don kaucewa afkuwar ambaliya.