Shugaban Kasa BolaTinubu zai kaddamar da fara ginin sabuwar hedkwatar hukumar zabe ta Kasa INEC a birnin tarayya Abuja.

Shugaban zai kadamar da fara ginin sabuwar hedkwatar ta INEC ne a ranar Talata mai zuwa a Unguwar Maitama da ke birnin.

Rahotanni daga hukumar raya birnn tarayya Abuja FCDA, sun tabbatar da cewa Ma’aikatar birnin tarayya Abuja FCTA ce za ta gudanar da aikin.
Rahotanin sun ce aikin zai lakume biliyoyin nairori, duk da babu cikakken bayani akan aikin.

Wani jami’a a hukumar raya birnin na Abuja ya ce duk kuwa da cewa hukumar ta INEC hukuma ce mai zaman kanta, amma ma’aikatar birnin tarayya Abuja na da hurumin yin gudanar da gyare-gyare a gine-ginen gidajen gwamnatin na Abuja, ciki kuwa harda fadar shugaban Kasa da Majalisun tarayya.

A wata wallafa da mai magana da yawun Ministan birnin ta Abuja Nyesom Wike Lere Olayinka ya fitar, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa aikin na Ma’aikatar birnin Abuja ce.

Olayinka ya kuma bayyana cewa a jira zuwa ranar da za a kaddamar da aikin, don jin kudaden da aikin zai lakume.

Leave a Reply

%d bloggers like this: