Shugaban Majalisar Wakilai Hon Tajudden Abbas ya bayyana cewa Al’ummarsu ta Jihar Kaduna ba su da wani zabi a yayin zaben shekarar 2027 illa shugaban Kasa Bola Tinubu.

Tajudden ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da Yawun shi Musa Krishi ya fitar.
Acewarsa a zaben na 2027 dukkan kuri’un mutane Jihar Kaduna na shugaba Bola Tinubu.

Tajudden ya bayaana hakan ne a yayin ziyarar aiki da shugaba Bola Tinubu ya kai jihar ta Kaduna a jiya Alhamis, inda ya kaddamar da manyan ayyuka uku da gwamnan Jihar Malam Uba Sani ya kammala.

Shugaban Majalisar ya kara da cewa al’ummar Jihar Kaduna sun shirya tsaf domin kara yawun kuri’unsu da suka jefawa shugaba Tinubu a zaben 2023 don samun kari a zaben 2027.
Sannan kuma Tajudden ya yabawa shugaban Tinubu bisa sake gina babban titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa kuma Kano, inda ya ce shugaban ya fitar da kuɗaɗen kammala titunan a yayin kasafin kuɗin shekarar 2025.