Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da ‘yan ta’adda suka kai a kananan hukumomin Bokkos da Mangu a Jihar Filato.

Rahotanni bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai harin ne a jiya Alhamis, a kauyen Manja da ke masarautar Chakfem a kananan hukumomin na Mangu da kauyen Tangur da ke Bokkos.

Rahotannin sun ce maharan sun kai hare-haren ne gurare daban-daban kananan hukumomin, inda da suka kai hari Kauyen Manja da yammaci,yayi da misalin karfe 9:00 na dare maharan suka kai hari Kauyen Tangur.

Wasu majiyoyi daga yankunan sun bayyana cewa da zuwan ‘yan bindigan suka bude wuta, tare da haurawagidajen mukane suna hallakasu daga bisani kuma suka tsere.

Majiyoyin sun kara da cewa maharan sun kashe mutane Goma a Bokkos, inda kuma suka hallaka bakwai a Mangu.

Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan Jihar ta Filato ba ta ce komai ba game da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: