Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa babu gazawa a cikin yin sulhu da ƴan bindigan da suka guduri aniyar watsar da makamansu a Jihar, tana mai cewa hakan hanya ce mai kyau da za ta haifarwa da Jihar dauwamamman zaman lafiya.

Gwamnatin ta yi wannan kalami ne bayan wani mai suna Basharu Altine Guyawa mai amfani da shafukan sada zumunta ya soki aniyar gwamnatin na yi sulhu da ƴan ta’addan.
Sai dai kuma bayan sukar mai bai’wa gwamnan Jihar shawara na musamman kan sha’anin tsaro Kanal Ahmed Usman Mai ritaya, ya bayyana cewa ba gazawa ce ta sanya gwamnatin jihar daukar matakin sulhu da ƴan bindigan ba sai don samar da zaman lafiya a fadin Jihar.

Acewar Kanal Usman ko wanne ɗan Kasa na da ƴancin faɗin albarkacin baka, amma ya zama wajibi su fito fili su bayyana irin yadda gwamnatin Jihar ke daukar matakai daban-daban a ciki kuwa harda yin sulhu da ƴan bindiga duk a kokarinta na magance matsalar rashin tsaro a Jihar.

Kazalika ya ce ya yi mataukar mamakin ganin yadda Basharu Guyawa ya soki yunkurin gwamnatin, yana mai cewa gwamnatin Jihar na amfani da bangarori biyu wajen magance matsalar.
Ya ce hanyoyin sun hada da jami’an tsaro da kuma tattaunawa da ƴan ta;addan.
Ya ce sakamaon matsalar ƴan bindigan al’umomin yankunan Isa, Sabon Birni, Rabah, Goronyo, tare da wasu yankunan na tserewa daga muhallansu, inda kuma manoma suma ke barin gonakins, wanda hakan ya haifar da karancin abinci da tsadar rayuwa a faɗin jihar.
Kanal Usman ya ce fatan gwamnatin Jihar dawo da zaman lafiya, farfado da harkokin nona, tare da mayar da mutane gidajensu.