Gwamnatin Jihar Anambra ta bai’wa mazauna birnin Jihar wa’adi su gyara gidanje su kafin ranar 1 ga watan Yuli mai kamawa.

Kwamishinan muhalli na Jihar Dr Filex Odimegwu ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.
Sanarwar ta ce dukkan wani gida da ya durkushe, ko suka lalace da su fante gidajen nasu kafin karewar wa’adin.

Kwamishinan ya ce hakan na daga cikin kudurorin gwamnatin Jihar na tsaftace dukkan lungu da sako na birnin Jihar, a kokarinta na kawata jihar musamman kan hanyoyin da mutane ke yin gini.

Kwamishinan ya ce guraren da ayyukan zai shafa sun hada da Onitsha, Awka, Nkpor Nnewi da Ekwuluobia.
Ya kara da cewa ya zama wajibi mutanen da ke wadanan guraren da su yiwa gidajensu fenti musamman waɗanda suka lalace a cikin shekaru goma da suka gabata.
Kazalika ya ce daga ranar 1 ga watan na Yuli hukumomin da abin ya shafa za su fara zagayawa domin ganin mutane sun bi dokar.