Jagororin jam’iyyun adawa a Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group NNCG na neman yin rajistar a jam’iyyar All Democratic Alliance ADA don zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita wajen tun karar jam’iyyar APC a zaben 2027.

A halin yanzu dai jagororin tafiyar sun mika wasika ga hukumar zabe mai zaman kanta ta Ƙasa INEC da ta yi musu rajista.
Takardar neman yin rijistar wadda aka aike da ita zuwa ga shugaban hukumar zabe na Kasa Farfesa Mahmood Yakubu a jiya Alhamis 19 ga watan Yuni.

Hukumar ta INEC ta karbi takardar a hukumance ne a yau Juma’a.

Shugaban Jam’iyyar ta ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanyawa takardar hannu, tare da mikata ga INEC don yi mata rijistar zamowa guda daga cikin jam’iyyu a Najeriya.
Jam’iyyar wadda ta kasance dauke da tambarin masara, inda kuma Takenta ya kasance Adalci ga kowa.
Jagororin hadar dai sun hada tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’i, Tsohonm gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi, tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata David Mark da dai sauransu.